Isa ga babban shafi
Najeriya - Chadi

Janyewar dakarun Chadi ya jefa mazauna Gajiganna cikin shakku

Rahotanni daga arewa maso gabashin Najeriya sun ce mazauna garin Gajiganna mai iyaka da tafkin Chadi da dama sun kauracewa muhallansu bayan janyewar dakarun Chadi dake taimakawa wajen yakar Boko Haram, bisa tsoron yiwuwar fuskantar hare-hare daga kungiyar.

Wasu daga cikin sojojin Chadi da sukai aikin tallafawa dakarun Najeriya wajen yakar Boko Haram a Borno.
Wasu daga cikin sojojin Chadi da sukai aikin tallafawa dakarun Najeriya wajen yakar Boko Haram a Borno. AFP
Talla

Wata majiya ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar mafi akasarin wadanda suke kauracewa muhallansu nasu sun tsere ne zuwa Maiduguri.

Wannan na zuwa ne bayan da a jiya asabar rundunar sojin kasarta Chadi ta sanar dajanye ilahirin dakarunta dubu 1 da 200 da suka shafe akalla watanni 9 suna yakar Boko Haram a Najeriya, saboda karewar wa’adin da aka dibar musu.

Sai dai Babban Hafsan rundunar sojin Chadi Janar Tahir Erda Tahiro, ya ce akwai yiwuwar sake tura wasu dakarun na Chadi zuwa Najeriya, domin ci gaba da aikin samar da tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.