Isa ga babban shafi

'Yan ta'adda sun kashe mutane 6 a arewa maso gabashin Najeriya

‘Yan ta’adda masu alaka da kungiyar IS sun kashe mutane 6, kana suka yi awon gaba da wasu 5 a yau Lahadi, a arewa maso gabashin Najeriya, bayan sun datse wata babbar hanya, suka kuma rika zaben jami’an tsaro da ma’aiaktan agaji, kamar yadda shaidun gani da ido suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa.

Sojojin Najeriya reke da tutar Boko Harm
Sojojin Najeriya reke da tutar Boko Harm REUTERS/Emmanuel Braun
Talla

AKalla mujahidan kungiyar IS reshen Afrika ta yamma su 30 ne suka karbe iko da babbar hanyar da ke kusa da kauyen Gasarwa, daga arewacin babban birnin jihar Bornon Najeriya.

‘Yan ta’addan sun tare matafiya ne, inda suke musu tambayoyi, daga nan ne suka tsame mutane 6 suka kashe su nan take, wasu ta harbin bindiga, wasu kuma yankan rago.

Wani direban bus da aka yi abin akan idanunsa ya ce, maharan sun bi wani dan sanda da ya yi yunkurin tserewa, inda suka kashe shi ta wurin taka shi da mota.

Sun tafi da wani dan sanda da wani ma’aikacin agaji.

Cikin wadanda maharan suka kashe har da wasu Fulani makiyaya, da mata biyu.

A ‘yan watannin baya rikici tsakanin ‘yan ta’adda da Fulani maakiyaya ya zafafa, inda suke yawan kai samame rugagen su suna kwashe musu dabbobi.

Ko a makon da ya gabata, makiyaya 19 ne wadannan ‘yan ta’adda suka kashe a tsakanin iyakar Najeriya da Kamaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.