Isa ga babban shafi
Najeriya-Lafiya

Illar cutar Noma da kuma rigakafin kamuwa da ita

Najeriya ta ware ranakun 18 ga watan Nuwamba kowace shekara, a matsayin ranar fadakar da jama’a kan cutar noma dake lalata fuska, inda ake gudanar da tarurrukan wayar da kan jama’a dangane da illar cutar da kuma yadda ake maganin ta.

Bilyaminu mai shekaru 20 mazaunin jihar Sokoto a Najeriya, daya ne daga cikin mutanen da suka yi fama da cutar noma dake lalata fuska. 13/4/2017.
Bilyaminu mai shekaru 20 mazaunin jihar Sokoto a Najeriya, daya ne daga cikin mutanen da suka yi fama da cutar noma dake lalata fuska. 13/4/2017. Claire Jeantet - Fabrice Caterini/INEDIZ
Talla

Kungiyar agaji ta Medicins Sans Frontier MSF, tare da ma’aikatar lafiyar Najeriya, sun hada kai wajen shawo kan wannan cuta.

Zuwa wannan lokaci kuma kungiyar agajin ta MSF, inda ta taimaka wajen yiwa mutane sama da 500 da suka kamu da cutar aiki daga shekarar 2015 zuwa yanzu domin ganin an gyara musu fuskokin su, a asibitin dake Sokoto.

Mulikat Okonlawo na daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin, bayan kamuwa da cutar, ga tsokacin da tayi mana akai.

Yayin zantawa da sashin Hausa na RFI ta ce daga cikin alamun farko na kamuwada cutar ta noma da ya kamata a maida hankali kawai, akwai zazzabi da kuma zafin jiki.

Kwararru kan lafiya sun bayyana rashin samun abinci mai gina jiki da kuma rashin tsafta a matsayin manyan abubuwan dake haddasa kamuwa da ce wannan cuta ta Noma, la’akari da cewar cutar na mamayar jikin dan adam ne a dai dai lokacin da karfin garkuwar jikinsa yayi kasa sosai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.