Isa ga babban shafi

An kashe mutane 2 a zaben Kogi

Akalla mutene 2 'yan bindiga sanye da kayan 'yan sanda suka kashe a Jihar Kogi dake Najeriya, daya daga cikin jihohin da ake zaben gwamna a yau. 

Akwantin zabe a Najeriya
Akwantin zabe a Najeriya
Talla

Yan bindiga sanye da kayan Yan Sanda suka kasha a karamar hukumar Dekina, inda ake gudanar da zaben Gwamna.

 

Shaidun gani da ido a karamar hukumar Dekina, inda lamarin ya auku, sun ce an kashe mutanen biyu Umoru Shuaivu da Faruk Suleiman ne a daidai lokacin da ake kada kuri’a.

A jihar Bayelsa ma an sanar da harbe harbe a mazabar Opolo, da ake zarin Yan bangar siyasa da aikatawa.

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kada kuri’ar sa a mazabar sa dake Otueke tare da uwargidan sa Patience.

Tun farko dai, rundunar ‘yan san dan kasar ta bayyana aikewa da jami’anta dubu 66 da 241, don tabbatar da doka da oda.

Daga cikin wannan adadi dai, rundunar ‘yan sandan tace dubu 35 da 200 an girke su ne a jihar Kogi, yayinda aka tura dubu 31 da 41 zuwa Bayelsa.

A Bayelsa ‘yan takara 45 ke fafatawa, inda ke sa ran hamayya za ta fi zafi tsakanin dan takarar PDP Douye Diri da Mista David Lyon na jam’iyyar APC. Yayinda a Kogi ‘yan takara 24 za su fafata, ciki har da gwamna mai ci Yahya Bello na APC da kuma dan takarar PDP Musa Wada.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.