Isa ga babban shafi

A Najeriya NECO ta kori ma'aikatan ta 70

Hukumar Kula da jarabawar kammala karatun Sakandare a Najeriya da akafi sani da suna NECO ta sanar da korar ma’aikatan ta 70 saboda mallakar takardun kammala karatu na bogi.

Hukumar da ke Kula da jarabawar kammala karatun Sakandare a Najeriya da akafi sani da suna NECO
Hukumar da ke Kula da jarabawar kammala karatun Sakandare a Najeriya da akafi sani da suna NECO RFI/Hausa
Talla

Shugaban sashen yada labarai na hukumar, Azeez Sani, yace an kori ma’aikatan ne bayan wani kwamitin tantance takardun ma’aikata ya kammala aikin sa da ya hada da gayyatar wadanda ake zargi domin kare kan su.

Sani yace wasu daga cikin ma’aikatan da kan su suka shaidawa kwamitin cewar takardun nasu na bogi ne, yayin da kwamitin ya kuma tintibi wasu makarantun da ma’aikatan suka ce sun kammala wadanda suka musanta basu takardun shaidar da suka gabatar.

Jami’in yace bayan kammala binciken, kwamitin ya mika rahotan sa ga hukumar wadda ta gabatarwa shugabannin gudanarwar ta domin nazari akai.

Sani yace taron hukumar gudanarwar na 17 ya amince da korar ma’aikatan 70 wadanda ya bayyana su a matsayin matakin farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.