Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya na fatan samun karin biliyoyin naira daga mai a 2021

Gwamnatin Najeriya ta ce tana sa ran samun karin kudaden shiga daga kamfanonin hakar mai, da akalla dala biliyan 1 da rabi, kwatankwacin naira biliyan 543 nan da shekarar 2021.

Wasu masu ruwa a tsaki a fannin man na fargabar cewa tilasta kara kudaden harajin ribar hakar man, ka iya sanya wasu kamfanoni ficewa daga Najeriya.
Wasu masu ruwa a tsaki a fannin man na fargabar cewa tilasta kara kudaden harajin ribar hakar man, ka iya sanya wasu kamfanoni ficewa daga Najeriya. AFP/PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Wannan hasashe ya biyo bayan matakin ‘yan majalisar kasar da a makon jiya suka sauya dokar tsarin rabon ribar danyen mai tsakanin kasar da manyan kamfanonin hako danyen mai a kasar.

Karkashin sabuwar dokar, dai kamfanonin man za su rika biyan gwamnatin Najeriyar harajin kashi 10 cikin 100 na jimillar ribar da da suke samu a shekara, muddin farashin gangar danyen man yana sama da dala 20, zalika za’a sake yiwa dokar rabon ribar man kwaskwarima abinda zai kai ga kara harajin da kamfanonin man za su rika baiwa Najeriyar idan farashin gangar danyen man ya zarta dala 150.

A shekarar 1993, aka soma kafa wannan doka, Sai dai duk da karuwar farashin gangar danyen tsawon shekaru, ba a sake yiwa dokar kwaskwarima ba, sai a wannan karo.

Sai dai wasu masharhanta na fargabar cewa matakin yiwa dokar rabon ribar hakon man ka iya sanya wasu kamfanonin man ficewa daga Najeriya.

Cikin watan Oktoba, gwamnatin Najeriya ta ce tana neman dala biliyan 62, daga wasu manyan kamfanonin hakar mai dake kasar, kudaden da ta ce ya kamata kamfanonin su biya ta a tsawon shekaru 20 da suka gabata.

Daga cikin Kamfanonin kuwa akwai Exxon Mobil, da kuma Shell.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.