Isa ga babban shafi
Najeriya-Zamfara

Sarakuna da jami'an tsaro na da hannu a matsalar tsaron Zamfara - Rahoto

Kwamitin da gwamnan Zamfara ya kafa domin gudanar da bincike kan masu hannu cikin hare-haren ‘yan bindiga da kuma barnar da matsalar ta tafka, ya gano wasu bata-garin jami’an ‘sojoji da yan sanda da kuma sarakunan gargajiya dake assasa matsalar.

Rahoton kwamitin bincike kan matsalar tsaro a Zamfara, ya ce 'yan bindiga sun karbi kudaden fansar da ya adadinsu ya zarta naira biliyan 3 cikin shekaru 8..
Rahoton kwamitin bincike kan matsalar tsaro a Zamfara, ya ce 'yan bindiga sun karbi kudaden fansar da ya adadinsu ya zarta naira biliyan 3 cikin shekaru 8.. REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo
Talla

A Juma’ar da ta gabata kwamitin dake karkashin jagorancin tsohon sifeta Janar na Yan Sandan Najeriya, Muhammad Abubakar ya mika rahoton binciken da ya tattara.

Rahoton ya bankado wasu sarakuna 5 gami da dagatai da masu unguwanni sama da 40 dake aiki tare da ‘yan bindiga a jihar ta Zamfara, sai kuma jami’an soji 10, da yan sanda da kuma wasu ma’aikatan gwamnati.

Rahoton kwamitin ya ce daga watan Yuni na shekarar 2011 zuwa watan Mayu na 2019 da muke ciki, yan bindiga sun karbi kudin fansar mutanen da suka sace da adadinsa ya zarta naira biliyan 3, daga sama da mutane dubu 3 da 600.

Yayin mika rahoton binciken, tsohon sifetan ‘yan Sandan Muhammad Abubakar ya ce hare-haren ‘yan bindigar daga 2011 zuwa 2019, tayi sanadin maraitar da kananan yara dubu 25 da 50, tare da raba wasu mutanen dubu 190 da 340 da muhallansu a cikin jihar Zamfara.

Rahoton ya kuma kara da cewa Fulani makiyaya sun rasa shanu sama da dubu 2, tumaki 141 da kuma awakai, jakuna da rakuma sama da dubu 2 da 500, sakamakon hare-haren nay an bindiga, yayinda aka tafka hasarar ababen hawa da suka hada da motoci da Babura sama da dubu 147 a tsawon shekaru 9 da bullar matsalar tsaron.

Cikin rahoton, tsohon sifeton yan sandan Najeriyar, ya shawarci gwamnati da cewar ta karbe iko da dukkanin gonakin da suka mamaye burtalolin shanu, sai kuma rungumar tsarin kiwo na zamani.

Kwamitin ya kuma shawarci gwamnatin Zamfara da ta hada gwiwa da jihohi makwabta wajen gayara hanyoyin da suka sada su, da kuma wadanda suka shiga kauyuka, domin saukakawa jami’an tsaro zirga-zirga da sauran jama’ar gari.

Zalika akwai bukatar yan bindiga su kwance damara ba tare da sharadi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.