Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotun Najeriya ta ba da umarnin sakin Sowore

Wata babbar kotun tarayya da ke birnin Abuja na Najeriya ta ba da umurnin gaggauta sakin mawallafin Jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore, wanda jami’an tsaro suka kama saboda jagorantar zanga-zangar adawa da gwamnatin kasar.

Omoyele Sowore.
Omoyele Sowore. DR/saharareporters.com
Talla

Alkalin kotun, Taiwo Taiwo ya ce, dokar kasa ta bai wa kowa damar gudanar da zanga-zangar lumana, kuma wa’adin umurnin da kotu ta bayar na ci gaba da tsare Sowore ya cika, saboda haka mai shari’a Taiwo ya ba da umurnin gaggauta sakin sa.

Sai dai alkalin ya bukaci Sowore da ya gabatar da takardun fasfo dinsa ga kotu, sannan kuma lauyansa Femi Falana ya sanya hannu domin amincewa da buktar sake bayyanar Sowore a duk lokacin da kotu ta bukace shi a zaurenta.

A ranar 3 ga watan Agustan da ya gabata ne aka kama Sowore bayan ya bukaci gudanar da zana-zangar a fadin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.