Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta zargi MDD da rashin adalci cikin sabon rahotonta kan kasar

Gwamnatin Najeriya ta yi Allah wadai da wani rahoton majalisar dinkin duniya kan matsalolin tsaro a kasar.

Dakarun sojin Najeriya a jihar Borno.
Dakarun sojin Najeriya a jihar Borno. REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo
Talla

Cikin wata sanarwa, kakakin shugaban Najeriya Malam Garba Shehu, ya ce rahoton na wakilyar majalisar dinkin duniya Agnes Callarmard, bai yi adalci ba, wajen fayyace gaskiyar halin da ake ciki kan tsaro a Najeriya ba.

Martanin na gwamnatin Najeriya, ya zo ne kusan makwanni 3, bayan wallafa rahoton.

Cikin rahoton, wakiliyar majalisar dinkin duniyar, ta bayyana Najeriya a matsayin kasar dake fama da rikicin cikin gida a sassanta da dama, wadanda ke dada kamari, ko da yake rahoton ya yabawa gwamnati kan nasarorin da ta samu kan Boko Haram.

A bangaren tashe-tashen hankula a sauran sassan kasar, rahoton majalisar dinkin duniyar ya bayyana rashin bibiya, talauci, sauyin yanayi da kuma yaduwar muggan makamai a tsakanin jama’a a matsayin wasu daga cikin matsalolin da ke rura wutar matsalolin tsaro da rikice-rikicen da Najeriya ke fuskanta.

Sauran matsalolin a cewar majalisar dinkin duniya sun hada da, yadda gwamnati ke yin amfani da karfi wajen dankwafe wasu kungiyoyi a Najeriyar da suka hada da ‘yan shi’a, ‘yan Kungiyar IPOB da aka haramta, da kuma al’ummar Ogoni.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta bayyana bacin rai kan yadda rahoto ya gaza bayyana matakan da take dauka wajen magance matsalolin da ya zayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.