Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Rashawa: An kwace kadarorin manyan jami'an hukumar kwallon kafar Najeriya

Hukumomi a Najeriya sun kwace kadarori mallakin manyan jami’en hukumar kwallon kafar kasar, har ma da na shugaban hukumar Amaju Pinnick a wata sabuwar tuhumar rashawa.

Shugaban Hukumar NFF, Amaju Pinnick tare da shugaban Hukumar FIFA, Gianni Infantino.
Shugaban Hukumar NFF, Amaju Pinnick tare da shugaban Hukumar FIFA, Gianni Infantino. REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo Supplied by Action Images
Talla

Jami’en hukumar yaki da rashawa ta ICPC sun karbe kadarori fiye da 12, wadanda rabin su na Amaju Pinnick ne, har ma da wani a birnin Landan.

Mai Magana da yawun hukumar ta ICPC Rasheedat Okoduwa, ta ce ana binciken da dama daga cikin jami’en hukamar kwallon kafar kasar, wadanda ta ce abin da suka mallaka sun fi karfin abin da suke samu a matsayin kudin shiga.

Ana tuhumar manyan jami’en NFF karkashin jagorancin Amaju Pinnick kan laifukan da suka jibanci rashawa har 3, har da laifin kin bayyana kadarorinsu da kuma yin kwanciyar magirbi a kan kudade da suka kai dala miliyan 8 da dubu dari 4 da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta biya Najeriya.

A ranar 26 ga watan Satumba za a ci gaba da sauraron karar.

A waje daya kuma an gurfanar da babban sakataren hukumar NFF din, Dr. Mohammed Sanusi da wasu akantoci uku na hukumar gaban kotu saboda zargin su da halin kuruciyar bera kan wasu miliyan 10 na dala da FIFA da CAF suka ba Najeriya gudummawa don bunkasa kwallon kafa a kasar.

A watan Yuli, hukumar kwallon kafa ta duniya ta salami Amaju Pinnick a matsayin mataimakin shugaban ta, biyo bayan zarginsa da laifin rashawa, wadda ya musanta, wadda hukumar ta NFF ke bayyana binciken a matsayin bita – da – kulli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.