'Yan Najeriya sun yi bore a ofishin jakadancin Birtaniya
Gamayyar Kungiyoyin Fararen Hula ta gudanar da gangami a harabar ofishin jakadancin Birtaniya da ke birnin Abuja na Najeriya domin nuna adawa da wani hukunci da wata kotun Birtaniya ta yanke kan Najeriya.
Wallafawa ranar:
Kotun ta umarci gwamnatin Najeriya da ta biya wani kamfanin tsibirin Ireland, P&ID zunzurutun Dala biliyan 9.6 sakamakon karya ka’idojin yarjejeniyar kwangilar da ke tsakanin bangarorin biyu.
Gamayyar kungiyoyin ta bayyana hukuncin a matsayin damfara kan Najeriya, yayinda masu zanga-zangar dauke da alluna suka yi biris da ruwan saman da ake tafka wa a birnin na Abuja.
Wasu daga cikin allunan na cewa, “ Najeriya da Birtaniya aminan juna ne, ba makiya ba ne”. “ ‘Yan Najeriya miliyan 200 ba su amince da hukuncin Birtaniya ba.” “ Hukuncin Dala biliyan 9.6 damfara ce”.
Wasu alkaluman na cewa, “ Boris Johnson , ka taimaka wa shugaba Buhari wajen yaki da cin hanci.”
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu