Najeriya ta samu nasarar ce bayan doke Kamaru da kwallaye 3-2 a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Da fari dai ‘yan matan na Najeriya da Kamaru sun kammala wasan a 1-1, bayan shafe mintuna 120 suna fafatawa, abinda ya kai ga bugun Fanareti.
Najeriya ta taba lashe kyautar Zinare a fagen kwallon kafar mata yayin wasannin motsa jikin nahiyar Afrika a shekarun 2003 da 2007.