Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 23/09 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 22/09 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 22/09 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 23/09 06h17 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 23/09 07h00 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 22/09 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 22/09 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 23/09 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 19/09 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 22/09 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 22/09 16h06 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 22/09 16h30 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 20/09 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 22/09 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 20/09 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 22/09 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 20/09 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 22/09 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 20/09 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Gaggauce

Rahotanni sun bayyana cewa harin farko ya faru ne a Bourzanga na yankin arewacin kasar lokacin da wani dan bindiga cikin dare ya bude wuta kan mutane tare da hallaka 6, yayinda wani harin na daban kuma ya lakume rayukan mutane 3.

Najeriya

Muna bibiyar karin 'yan damfara baya ga wadanda FBI ke nema - EFCC

media Hukumomin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya sun bayyana cewa tuni suka kame mutane 28 kari kan wadanda hukumar FBI can a Amurka ta kame AFP Photo/MOHD RASFAN

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC, ta ce tana bibiyar wasu karin manyan ‘yan damfara, baya ga kusan guda 80 ‘yan Najeriya, da hukumar binciken laifuka ta Amurka FBI ta wallafa sunayensu.

Ofishin hukumar ta EFCC dake garin Ibadan ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai, inda tace yanzu haka jami’anta sun yi nasarar bankado wani asusu mai kunshe da akalla naira miliyan 223, da ‘yan damfarar suka samu ta hanyar kutsawa cikin bayanan sirrin da suka shafi asusun ajiya da kuma bayanan mutane daban daban a shafukansu na intanet.

Tuni dai hukumar ta EFCC ta bayyana kame mutane 28 daga cikin ‘yan damfarar da ake neman ruwa a jallo, bayan da suka yi awon gaba da miliyoyin dalolin Amurkawa.

A makon jiya hukumar binciken laifuka ta Amurka FBI ta wallafa sunayen ‘yan Najeriya kusan 80 da ta samu da laifin damfarar mutane dalar Amurka sama da miliyan 40, a tsakanin shekarun 2014 zuwa 2018, ta hanyar yanar gizo.

Yayin da ya ke karin bayani kan halin da ake ciki, shugaban hukumar na shiyyar Legas Muhammad Rabo, ya shaidawa manema labarai cewa, bayan hadin gwiwa da jami’an hukumar ta FBI, zuwa yanzu sun yi nasarar kame mutane 28 daga cikin ‘yan damfarar da Amurka ke farauta, yayinda suka kwato naira miliyan 486 daga hannunsu.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure