Saurare Saukewa Podcast
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 13/10 06h00 GMT
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 14/10 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 13/10 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 14/10 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 13/10 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 14/10 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 13/10 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 14/10 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 14/10 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 13/10 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 13/10 16h06 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 13/10 16h30 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 14/10 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 13/10 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 14/10 16h40 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 14/10 20h00 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 13/10 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 13/10 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 11/10 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Najeriya

EFCC ta soma bincikar Obasanjo kan salwantar dala biliyan 16

media Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo. Getty Images

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC, ta soma bincike kan shirin samar da wutar lantarkin da ya lakume dala biliyan 16 a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo.

Majiyoyin hukumar ta EFCC, sun ce za kuma a tuhumi wadanda suka jagoranci ayyukan shirin samar da lantarkin a lokacin shugabancin na Obasanjo, zalika binciken zai kuma fadada zuwa kan yan kwangilar da suka gudanar da ayyukan lantarkin a zamanin gwamnatocin marigayi Umaru Musa Yar’Adua da kuma Goodluck Jonathan.

Hukumar ta EFCC za ta kuma tuhumi wasu tsaffin ministocin Najeriya biyu da ba’a bayyana sunayensu ba, da kuma wasu tsaffin manyan jami’an gwamnatin kasar 18, da na babban bankin kasar CBN.

A karshen watan Yuli, majalisar wakilan Najeriya ta cimma matsayar gudanar da bincike dangane da makudan kudaden da gwamnatin tarayya ta biya kan kwangilolin magance matsalar rashin tsayayyar hasken lantarki a kasar.

Majalisar ta ce za a binciki tsohuwar gwamnatin da Olusegun Obasanjo ya jagoranta daga 1999 zuwa 2007, don bada bahasi kan dala biliyan 16 da gwamnatin yai ikirarin kashewa kan inganta wutar lantarkin.

A waccan lokacin, tsohuwar gwamnatin ta ce zuba makudan kudaden a fannin lantarkin zai samarwa da Najeriya karfin wutar da zai kai Megawatts dubu 40 a shekarar 2020.

Har yanzu dai samar da hasken lantarki batu ne da ‘yan siyasar Najeriya ke amfani da shi wajen neman kuri’a yayin yakin neman zabe, duk da ikirarin gwamnatocin da suka gabata, na zuba makudan kudade a fannin, ba tare da an ga sahihin sakamako ba.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure