Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotun Najeriya ta bayar da umarnin ci gaba da tsare Sowore

Babbar kotun tarayya da ke birnin Abuja na Najeriya, ta bai wa Hukumar Tsaron Farin Kaya, DSS umarnin tsare jagorar zanga-zangar juyin juya hali karkashin kungiyar RevolutionNow, wato Omoyele Sowore har tsawon kwanaki 45 kafin kammala bincike a kansa.

Omoyele Sowore
Omoyele Sowore DR/saharareporters.com
Talla

Mai shari’a Taiwo Taiwo ne ya bayar da umarnin, inda ya ce, za a iya sabonta  kwanaki 45 din muddin ba a kammala gudanar da bincike kan zargin Omoyele da aikata ta’addanci ba.

Wasu hujjoji da Hukumar DSS ta gabatar wa kotun sun hada da hoton bidiyon da ke nuna Sowore na ganawa da Nnamdi Kanu, yayinda wani hoton bidiyon ya nuna wasu kalamansa da ke cewa, za su hada hannu da haramtacciyar Kungiyar ‘Yan Shi’a domin gurgunta gwamnatin kasar.

DSS ta ce, an kama Sowore ne saboda shirya zanga-zangar juyin juya halin da ya kira a duk fadin Najeriya da zummar nuna rashin amincewa da salon mulkin kasar.

Sowore shi ne mawallafin jaridar Sahara Reporters da ake wallafawa a yanar gizo,sannan ya tsaya takarar shugaban kasar karkashin jam’iyyar African Action Congress a zaben 2019 da shugaba Buhari ya lashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.