Kotun ta bada umarnin maido da Shiekh Zakzaky Najeriya domin ci gaba da fuskantar shari’a, da zarar asibitin da yaje sun sallame shi.
Yayin yanke hukuncin, mai Shari’a Darius Khobo, ya ce jagoran na mabiya Shi’a zai tafi neman lafiyar zuwa Indiya ne tare da rakiyar jami’an gwamnatin Najeriya.
A lokuta da dama cikin makwannin da suka gabata, an yi arrangama tsakanin jami’an tsaron Najeriya, da ‘ya’yan kungiyar ta ‘yan uwa Musulmi a birinin Abuja, inda suka gudanar da zanga-zangar neman sakin shugabansu dake tsare don nema masa lafiya.
Shiekh Ibrahim Zakzaky da matarsa Zeenat, na daga cikin daruruwan ‘yan kungiyar IMN ta ‘yan uwa Musulmi da jami’an tsaron Najeriya suka kema cikin shekarar 2015, bayan arrangamar da aka yi tsakaninsu da mabiya jagoran na Shi’a a garin Zaria.