Kungiyar Shi'a za ta kalubalanci gwamnati a kotu
Yau ne Kungiyar Islamic Movement in Nigeria da aka fi sani da Shi’a za ta shigar da kara a babban kotun tarayya da ke birnin Abuja domin kalubalantar matakin gwamnatin kasar na haramta gudanar da ayyukanta.
Wallafawa ranar:
Babban Lauya mai rike da mukamin SAN, wato Femi Falana wanda ya dade yana kare shugaban kungiyar ta Shi’a Ibrahim El-Zakzaky, ya tabbatar da shirin kungiyar na zuwa kotun a yau Alhamis.
Wannan na zuwa ne jim kadan da kungiyar ta bayyana cewa, ta dakatar da zanga-zangar da take gudanarwa wadda ta rikide ta koma tarzoma a baya-bayan nan.
Mai magana da yawun kungiyar, Ibrahim Musa ya ce, sun dakatar da zanga-zangar ce domin bude sabuwar kofar lalubo hanyar samun masalaha tsakaninsu da gwamnati.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu