Isa ga babban shafi
Najeriya

Majalisa za ta binciki Obasanjo, 'Yar Adua, Jonathan da Buhari kan lantarki

Majalisar wakilan Najeriya ta cimma matsayar gudanar da bincike dangane da makudan kudaden da gwamnatin tarayya ta biya kan kwangilolin magance matsalar rashin tsayayyar hasken lantarki a kasar.

Tsaffin shugabannin Najeriya, Olusegun Obasanjo, marigayi Umar Musa Yar Aduwa da Goodluck Jonathan.
Tsaffin shugabannin Najeriya, Olusegun Obasanjo, marigayi Umar Musa Yar Aduwa da Goodluck Jonathan. Sahara Reporters
Talla

Daya daga cikin ‘yan majalisar wakilan Honorable Sada Soli Jibia ne ya gabatar da kudurin a wannan Alhamis, da ya samu amincewar daukacin takwarorinsa.

Majalisar ta ce za a binciki tsohuwar gwamnatin da Olusegun Obasanjo ya jagoranta daga 1999 zuwa 2007, don bada bahasi kan dala biliyan 16 da gwamnatin yai ikirarin kashewa kan inganta wutar lantarkin.

Binciken majalisar wakilan zai kuma fadada bin kwakkwafin zuwa kan gwamnatocin marigayi Umar Musa ‘Yar Adua, Goodluck Jonathan da kuma gwamnatin mai ci karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari.

A shekarar 2008 majalisar wakilan Najeriya ta taba kaddamar da bincike kan dala biliyan 16 da tsohon shugaban kasar Obasanjo yayi ikirarin kashewa don inganta lantarki ba tare da ikirarin ya tabbata ba.

A waccan lokacin, tsohuwar gwamnatin ta ce zuba makudan kudaden a fannin lantarkin zai samarwa da Najeriya karfin wutar da zai kai Megawatts dubu 40 a shekarar 2020.

Har yanzu dai samar da hasken lantarki batu ne da ‘yan siyasar Najeriya ke amfani da shi wajen neman kuri’a yayin yakin neman zabe, duk da ikirarin gwamnatocin da suka gabata, na zuba makudan kudade a fannin, ba tare da an ga sahihin sakamako ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.