Rahoton musamman kan cika shakaru 10 da rikicin Boko Haram kashi (7)

A ci gaba da kawo muku jerin rahotanni da hirarraki kan cika shekaru 10 da barkewar rikicin Boko Haram, a wannan karon mun waiwayi hirar da muka yi da shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai a birnin Maiduguri na jihar Borno a karshen shekarar da ta gabata, inda ya bayyana irin ayyukan da sojojin kasar ke yi na kakkabe 'ya'yan kungiyar. Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar.