Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 28/02 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 28/02 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 28/02 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 28/02 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 28/02 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 28/02 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 28/02 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 28/02 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 28/02 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Najeriya

An kashe dan sanda da mai bautar-kasa a rikicin 'yan Shi'a

media Masu zanga-zangar na bukatar gwamnatin Najeriya da ta saki jagoransu, Sheikh Ibrahim Zakzaky, REUTERS/Afolabi Sotunde

An tabbatar da mutuwar Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sandan Najeriya, Usman Umar da wani matashi bai bautar-kasa, Precious Owolabi sakamakon raunin bindigar da suka samu a sabuwar tarzomar mabiya akidar Shi’a da ta barke a birnin Abuja a ranar Litinin.

Bayanai na cewa, masu zanga-zangar ne suka harbe Mataimakin Kwamishinan 'Yan sandan, yayinda ya rasu a daidai lokacin da yake karbar magani a asibiti.

Shi kuwa Owolabi mai shekaru 23 da ke hidimar kasa a gidan talabijin na Channels, a cikin daren da ya gabata ne aka tabbatar da mutuwarsa bayan harsashin bindiga ya same shi a daidai lokacin da yake bakin aikin daukar rahoton arangamar tsakanin ‘yan sanda da ‘yan Shi’a.

A bangare guda mai magana da yawun Kungiyar ‘yan Shi’a a Najeriya, Ibrahim Musa, ya bayyana cewa, an kashe musu mabiya akalla 11, yayinda aka raunata da dama daga cikin su.

Mabiyan Shi’ar dai sun gudanar da zanga-zangar ce da zummar matsin lamba kan gwamnati don ganin ta saki jagoransu,Sheik Ibrahim Zakzaky da ke tsare.

Tuni jamai’an tsaro suka kama mutane da dama da ake zargin alakarsu da masu zanga-zangar.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure