Daya daga cikin lauyoyin masu gabatar da karar Chris Uche SAN, yace sun gayyaci shaidu 8 ne a wannan Juma’a domin bada bayani kan abinda suka sani na zargin tafka magudi a zaben shugabancin kasar da ya gabata.
Lauyan ya ce a lokacin da lamarin ya auku, shaidun nasu na kan hanyar zuwa Abuja ne daga jiharZamfara.
Ana sa ran cewa kotun sauraron kararrakin zaben shugabancin na Najeriya karkashin jagorancin mai shari’a Muhammed Garba za ta ci gaba da zama a makon gobe, lokacin da shaidun da PDP ke gabatarwa za su cika 36, kamar yadda lauyoyin masu kara suka nema.
A nasu bangaren lauyoyin masu kare wadanda ake kara sun bukaci kotun ta yi watsi da bukatar lauyoyin PDP da dan takararta na dage zaman zuwa mako mai kamawa.