za a gurfanar da tsohon ministan sadarwar Najeriya Lai Muhamed a gaban Kotu
Hukumar dake yaki da cin hanci ta Najeriya ICPC, tace za ta gurfanar da tsohon ministan yada larabai Lai Mohammed a gaban kotu, domin yin bayani kan yadda Hukumar sadarwar kasa ta kashe naira biliyan 2 da rabi na kudaden da gwamnati ta hanyar da bai kama ta ba.Mai magana da yawun hukumar Rasheedat Okoduwa, ta tabbatar da shirin gurfanar da tsohon ministan a shari’ar da aka yiwa Darakta Janar na hukumar sadarwa Ishaq Modibbo Kawu, na kashe kudaden wajen bada kwangilar da ta saba ka’ida.Tuni ICPC ta gurfanar da Kawu da wasu jami’an hukumar sadarwar a gaban kotu, inda ake tuhumar su da laifuffuka 12 ciki harda yaudarar ministan wajen amincewa da wani kamfani mai zaman kan sa domin yin kwangilar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar: