Isa ga babban shafi
Najeriya-Birtaniya

Birtaniya ta gargadi al'ummar kan ziyartar jihohin Najeriya 21

Kasar Birtaniya ta gargadi al’ummarta da ke zaune a Najeriya ko kuma aiki ya kai su kasar da su yi taka-tsan-tsan da ziyartar wasu jihohin kasar 21 ciki har da Delta a kudancin kasar mai fama da hare-haren ‘yan bindiga da kuma Borno mai fama da rikicin Boko Haram.

Cikin bayananta Birtaniyar ta alakanta gargadin da yadda ayyukan garkuwa da mutane ke ci gaba da ta'azzara a sassan Najeriyar
Cikin bayananta Birtaniyar ta alakanta gargadin da yadda ayyukan garkuwa da mutane ke ci gaba da ta'azzara a sassan Najeriyar NAN
Talla

Cikin wata doguwar takadda mai dauke da shawarwari ga al’ummar Birtaniyar a Najeriya, kasar ta bukaci al’ummarta su kasance cikin taka-tsan-tsan tare da bukatar cikakken rakiyar jami’an tsaro a duk lokacin da ziyarar dole ta kama su zuwa jihohin 21.

A cewar Birtaniya matakin gargadin al’ummar na ta ya biyo bayan tsanantar ayyukan ta’addanci a sassan Najeriyar da suka kunshi hare-haren Boko Haram a arewa maso gabashi da hare-haren ‘yan bindiga a yankin arewa maso yammaci baya ga hare-haren tsageru a kudu maso kudancin kasar.

Haka zalika Birtaniyar ta jadadda gargadi kan yadda annobar cutar Lassa ke kara ta’azzara a wasu sassan Najeriyar baya ga barazanar iya fuskantar kwayar cutar Zika a wasu yankuna.

Sauran jihohin da Birtaniyar ta gargadi al’ummar ta da ziyara baya ga Borno akwai jihar Yobe ka na Adamawa sai jihar Gombe da Delta, haka zalika Bayelsa da jihar Rivers sannan Akwa Ibom da Cross River baya ga jihar Zamfara.

Sauran jihohin Najeriyar da ke fuskantar matsalar tsaro a cewar Birtaniyar sun hada da Bauchi da jihar Kano da Kaduna sannan Jigawa da Katsina kana Kogi da Sokoto sai Kebbi Delta da Bayelsa da kuma jihar Abia.

Cikin jawaban na Birtaniya ta kuma bayyana yiwuwar fuskantar hare-hare a jihohin Gombe Kano Kaduna da Jos ka na da Bauchi baya ga Abuja babban birnin Najeriyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.