Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan kunar bakin wake sun kashe mutane a Borno

Akalla mutane 30 sun rasa rayukansu a wasu jerin hare-haren bama-bamai da aka kaddamar a wani kauyen jihar Bornon Najeriya a cikin daren da ya gabata.

Harin kunar bakin wake ya hallaka mutane 17 a jihar Bornon Najeriya
Harin kunar bakin wake ya hallaka mutane 17 a jihar Bornon Najeriya Daily Trsut
Talla

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, lamarin ya faru ne a kauyen Mandarari da ke Karamar Hukumar Konduga da misalin karfe 8:50 a daren da ya gabata.

Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kaddamar da harin, amma ana kyautata zaton harin ya yi kama da na mayakan Boko Haram.

Majiyoyi sun ce, wasu ‘yan kunar bakin wake uku ne suka tayar da bama-baman da suka yi damara da su a wani gidan kallo da ke kauyen.

Harin ya kuma raunata mutane akalla 30, yayinda bayanai ke cewa, wani jami’in ‘yan sandan sintiri guda na cikin wadanda harin ya kashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.