Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 20/11 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/11 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/11 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 20/11 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/11 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 20/11 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/11 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 20/11 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 19/11 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/11 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/11 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 19/11 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/11 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/11 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 19/11 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/11 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 19/11 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/11 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 19/11 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Najeriya

Abubuwan da Buhari zai mayar da hankali a kai a wa'adi na biyu

media Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a lokacin da yake karbar rantsuwar kama aiki a wa'adinsa na biyu REUTERS/Afolabi Sotunde

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake jaddada aniyarsa ta bunkasa tattalin arzikin kasar da kuma yaki da matsalar ta’addanci.

A yayin jawabin bikin ranar dimokiradiyar da aka gudanar a birnin Abuja wanda ya samu halartar daruruwan mutane cikinsu har da shugabannin kasashen Afrika da wakilan kasashen duniya, Buhari ya ce, ayyukan ta’addanci da matsalar tsaro sun zama ruwan dare, amma gwamnatinsa za ta ci gaba da jajircewa wajen shawo kan matsalar.

Shugaba Buhari ya bayyana yadda alkiblar gwamnatinsa ta yanzu za ta kasance da suka hada da zakulo shahararrun 'yan Najeriya da abokansu domin aiwatar da manufofin gwamnati.

Daga cikin manufofin har da inganta manyan makarantu da cibiyoyin bincike domin sanya Najeriya a sahun gaba wajen fasahar zamani da kuma kara zuba jari wajen harkar bada lafiya daga matakin farko zuwa na karshe da horar da ma’aikatan lafiyar da kuma samar da kayan aiki na zamani.

Dangane da noma da samar da abinci, shugaba Buhari ya ce, manoman Najeriya sun taka rawar gani wajen samar da shinkafa da masara da rogo da kaji da taki da kuma iri, saboda haka gwamnati za ta taimaka musu ta hanyoyi daban daban don ganin sun fitar da amfanin gonarsu zuwa kasashen duniya.

Buhari ya bayyana damuwa kan yadda ake sare itatuwa domin samun makamashi wanda ke yi wa dazukan kasar illa, inda yake cewa abin takaici ne kasar da ke fitar da ton miliyan 2 na iskar gas da ake girki da shi, bata iya amfani da rabin ton miliyan guda, abinda ya zama dole gwamnati ta dauki matakin gyara domin ganin jama’a sun rungumi iskar gas.

Shugaban kasar ya ce, yanzu haka gwamnati na gudanar da aikin gina hanyoyi da gadaje a sassa daban daban na kasar da suka kai kilomita 2,000, domin taimaka wa jama’a a harkar sufuri da kuma fitar da amfanin gonaki, yayinda a bangare daya kuma ake aikin gina layin dogo da tashoshin jiragen sama domin inganta harkar sufuri.

Buhari ya bayyana cewar, arzikin iskar gas da Najeriya ke da shi ya zarce na man fetur, yayinda kasar ta zama mai fitar da sinadarin yuriya da ake sarrafawa daga iskar gas, a daidai lokacin da gwamnati ke bukatar masu zuba jari domin inganta wannan bangaren.

A karshe shugaban kasar ya gargadi daidaikun mutane da kungiyoyin da ke yi wa jama’ar kasar barazana ko kuma masu sace dukiyar kasa domin azurta kansu tare da masu tinzira talakawa domin tada hankali, inda yake cewa lallai za su gamu da fushin hukuma.

Buhari ya ce gina kasa na daukan dogon lokaci, kuma a shirye suke su tabbatar da cewar Najeriya ta yi aiki yadda kowa zai ci moriyar ta.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure