Isa ga babban shafi
Najeriya

Musa, Iwobi da Abdullahi sun isa sansanin Super Eagles

Manyan ‘yan wasan babban tawagar kwallon kafar Najeriya, Ahmed Musa, Alex Iwobi da Shehu Abdullahi sun isa sansanin tawagar Super Eagles a otel din Golden Tulip dake Asaba ta jihar Delta.

Babbar tawagar kwallon kafar Najeriya, Super Eagles
Babbar tawagar kwallon kafar Najeriya, Super Eagles Reuters/Peter Cziborra
Talla

Da maraicen jiya Laraba ne wadannan ‘yan wasa uku suka sauka, wadda hakan ya kai jimillar ‘yan wasan da ke sansanin 23, ana kumasa ran dan wasan baya na Udinese, William Troost Ekong ya sauka a kowane lokaci daga yanzu.

A ranar Asabar nan mai zuwa tawagar ta Super Eagles din zata barje gumi a wasan sada zumunta da Zimbabwe, a filin wasa na Stephen Keshi da ke Asaba, duk a cikin shirin tunkarar gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2019 da za ta gudana a Masa.

Bayan wasan, ana sa ran kocin tawagar kwallon kafar Najeriyan, Gernot Rohr ya bayyana sunayen ‘yan wasa 23 da zasu wakilci kasar a gasar ta nahiyar Afirka.

Tawagar zata baro Najeriya zuwa garin Ismaila ta Masar a Lahadi mai zuwa, don ci gaba da shirye shiryen yin gumurzu a gasar,inda zata hadu da Burundi, Guinea da Madagascar a rukunin B.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.