Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan Najeriya miliyan 91 na fama da bakin talauci - Rahoto

Wani rahoton hadin gwiwar bankin duniya, asusun bada lamuni na duniya IMF da kuma majalisar dinkin duniya, ya ce mutane miliyan 91 ke fama da matsanancin talauci a Najeriya.

Masana sun yi hasashen cewa a kowane minti daya, akwai ‘yan Najeriya akalla 6 da suke afkawa cikin bala’in talauci.
Masana sun yi hasashen cewa a kowane minti daya, akwai ‘yan Najeriya akalla 6 da suke afkawa cikin bala’in talauci. AFP
Talla

Sabuwar kididdigar ta nuna cewa a halin yanzu rabin al’ummar Najeriya talauci yayiwa katutu, bayan samun Karin ‘yan kasar kusan miliyan 5 da suka fada kangin matsanancin talauci daga 2018 zuwa bana.

Kididdigar ta kara da hasashen cewa a kowane minti daya, akwai ‘yan Najeriya akalla 6 da suke afkawa cikin bala’in talauci.

A watan Yuni na shekarar bara, rahoton na masana tattalin arziki ya bayyana Najeriya a matsayin hedikwatar talauci ta duniya, sakamakon adadin masu fama da talauci matsananci da ya kai miliyan 87, zalika rahoton yayi la’akari da girman gibin da ke tsakanin miliyoyin talakawan kasar da kuma tsirarun attajirai.

Sai dai a waccan lokacin, shugaban Najeriya Muhammadu yayi watsi da rahoton hadin gwiwar na bankin duniya, duk da cewa Fira Ministar Birtaniya Theresa May ta yadda da sahihancinsa, la’akari da yadda ta buga misali da rahoton, yayin gabatar da wani jawabi.

Masana tattalin arziki, sun ce zuwa ranar 13 ga watan Fabarairu na 2019 da ya gabata, jimillar ‘yan Najeriya miliyan 91 masu fama talaucin na rayuwa ne kan kasa da dala daya kwatankwacin naira 360. Yayinda kuma kwararrun na tattalin arziki suka bayyana duk wanda baya iya samun kwatankwacin naira 693 a rana, a matsayin mai fama da matsanancin talauci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.