Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya sun kame karin gungun masu garkuwa da mutane

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun cafke wani gungun masu garkuwa da mutane, da suka addabi kauyukan da ke yankin Funtua zuwa Faskari a jihar Katsina.

Wasu dakarun sojin Najeriya.
Wasu dakarun sojin Najeriya. REUTERS/Joe Brock
Talla

Kakakin sojin Najeriyar Kanal Sagir Musa, ya ce dakarun sun kame gungun da ya kunshi mutane 5, a samamen da suka kai kan kauyen Sheme, da kuma dajin Ruwan Godiya.

Kanal Musa ya kara da cewa, yayin amsa tambayoyi, masu laifin sun amsa cewa tabbas suna da hannu a mafi akasarin sace mutane da kuma yin garkuwa da su, da ake yi a kauyukan na yankin Funtua zuwa Faskari, inda suke mika wadanda tsautsayi ya fada musu zuwa, manyan jagororinsu da ke kuryar dajin Ruwan-Godiya.

A watan mayu da ya gabata, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kame masu garkuwa da mutane 93 da tarin makamai, da ke cikin ‘yan bindigar da suka addabi jama’a da sata da kuma yin garkuwa da su, a jihohin Niger, Katsina da kuma Kaduna, da kuma kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Kakakin rundunar ‘yan sandan DCP Frank Mba, ya ce sun yi nasarar damke ‘yan bindigar ne, bayan shafe makwanni biyu suna kai samame kan maboyar maharan lokaci guda a jihohin na Kaduna, Katsina da kuma Niger.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.