Isa ga babban shafi
Najeriya

Mabiya Shi'a sun zargi 'yan sanda da jikkata mabobinsu

Kungiyar ‘yan uwa Musulmi da aka fi sani da Shi’a, ta zargi ‘yan sandan a jihar Kaduna da ke Najeriya, da jikkata mabiyanta da dama, tare da kame wasunsu, yayinda suke tattakin ranar Kudus da suka saba yi duk shekara, domin alhinin ukubar da Falasdinawa ke fuskanta daga Isra’ila.

Wasu mabiya kungiyar ‘yan uwa Musulmi da aka fi sani da Shi’a, yayin zanga-zangar neman sakin jagoransu Sheikh Ibrahim Zakzaky a Abuja.
Wasu mabiya kungiyar ‘yan uwa Musulmi da aka fi sani da Shi’a, yayin zanga-zangar neman sakin jagoransu Sheikh Ibrahim Zakzaky a Abuja. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Yayin ganawa da Manema Labarai a Juma’ar nan, kakakin mabiya Shi’ar Ibrahim Musa, yace suna gudanar da tattakin nasu ne cikin kwanciyar hankali da lumana, amma yan sanda suka soma jefa musu barkonon tsohuwa gami da harbi da bindiga.

Musa ya kuma kara da cewa, tun kafin soma tattakin na ranar Kudus, jami’an tsaron ke sintiri a tituna cikin shirin ko ta kwana.

Kawo yanzu dai babu Karin bayani kan adadin wadanda suka jikkata, da kuma wadanda ke hannun jami’an tsaro, zalika rundunar ‘yan sandan ta Kaduna bata ce komai ba dagane da zargin da akai mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.