Kamfanin MTN ya kammala biyan tarar naira biliyan 330 a Najeriya
Kamfanin Sadarwa na MTN mallakin Afrika ta Kudu, ya biya kashin karshe na tarar biliyoyin nairar da gwamnatin Najeriya ta yanka masa, a dalilin saba ka’idar rashin yiwa miliyoyin layukansa rijista, ko kuma katse layukan da ba'a yiwa rijistar ba.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A kashin karshen dai kamfanin na MTN ya biya gwamnatin Najeriya naira biliyan 55, abinda ya bashi damar kammala biyan tarar ta naira biliyan 330 da hukumar kula da sadarwar kasar NCC ta yanka masa a shekarar 2016.
Da fari dai a watan Oktoban 2015 hukumar ta NCC ta yankawa MTN biyan tarar naira Tiriliyan 1 da doriya ne, saboda laifin kin katse layukansa akalla miliyan 5 da ba a yiwa rijista ba, duk da cewa gwamnatin Najeriya ta baiwa ilahirin kamfanonin sadarwar da ke kasar umarnin yin hakan, to amma daga bisani a 2016 aka sassauta tarar zuwa naira biliyan 330.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu