Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnoni ba su da ikon magance matsalolin tsaro - Ishaku

Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, ya jaddada bukatar kafa rundunonin ‘yan sanda a jihohin Najeriya, matakin da ya ce zai bada muhimmiyar gudunmawa wajen kawo karshen matsalar tsaron da ke girmama.

Gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku.
Gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku. Pulse.ng
Talla

Gwamnan na Taraba da ke ganawa da manema labarai a garin Jalingo ya ce a halin da ake ciki, gwamnoni ba su da wata muhimmiyar gudunmawa da za su bayar wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar al’umma, la’akari da cewa dukkanin rundunonin ‘yan sanda da na sojin Najeriya, suna karkashin gwamnatin tarayyar kasar ne a dunkule.

Ishaku ya kuma yi ikirarin cewa, duk wani gwamna da ce zai iya daukar mataki kan matsalolin tsaron da ke addabar jiharsa, zuki-ta-malle ce kawai ya sharara.

Dan haka gwamnan jihar na Taraba, ya bukaci shugabannin da abun ya shafa da kuma sauran ‘yan Najeriya su goyi bayan kasafta rundunar ‘yan sandan Najeriya zuwa karkashin jihohi.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da a Najeriya wani gwamna ke ikirarin cewa ba zai iya magance matsalolin tsaron da ke addabar jiharsa ba.

A watan Yunin shekarar 2018, gwamnan jihar Zamfara, kuma shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya a waccan lokacin, Abdul-Aziz Yari, ya bukaci majalisun tarayyar kasar da su cire wa gwamnoni mukamin da aka lakaba musu na zama shugabannin jami’an tsaron jihohinsu.

Yari ya ce gwamnonin basu da bukatar wannan mukami, la’akari da cewa basu da cikakken ikon sarrafa jami’an tsaron da ke jihohinsu, ta hanyar hukuntawa, kora ko kuma daukar sabbin jami’an tsaron, duk da cewa suna amsa mukamin shugabannin jami’an tsaron jihohin nasu.

Gwamnan jihar ta Zamfara ya bayyana haka a lokacin da ya ke nuna bacin ransa kan yadda har yanzu ake ci gaba da samun hasarar rayuka a jihar, sakamakon hare-haren ‘yan bindiga, duk da aikewa da karin jami’an tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.