Isa ga babban shafi
Najeriya

Yan sanda sun sake kame masu garkuwa da mutane sama da 70

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bayyana nasarar sake kame masu satar mutane da yin garkuwa da su sama 70 da suka addabi jama’a a sassan jihar Katsina da makwabtanta.

Dakarun rundunar 'yan sandan Najeriya.
Dakarun rundunar 'yan sandan Najeriya. Daily Post Nigeria
Talla

Yayin karin bayani ga manema labarai kan nasarar da suka samu, kwamishinan ‘yan sanda a jihar ta Katsina, Sanusi Buba, ya ce sun kwace tarin makamai da suka kunshi, bindigogi kirar AK 47 guda 43, bindigogi kirar gida ta harbi ka ruga guda 19, sai kuma manya masu sarrafa kansu guda 2 da kananan bindigogin 2.

Yan sandan sun kuma kwace harsasai sama dubu 1 da 500, Babura 44 da kuma motoci 5, sai kuma kayayyakin abinci da wasu Karin kayan da ‘yan bindigar ke amfani da su.

Cikin wadanda aka kama, akwai ‘yan bindigar da suka sace Hauwa Yusuf mai shekaru 80, suruka ga gwamnan jihar Aminu Bello Masari.

Idan za’a iya tunawa, ranar 9 ga watan Maris na 2019, ‘yan bindigar suka sace Hauwa, yayin da ake kan gudanar da zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisu. Masu garkuwa da mutanen kuma basu sake ta ba, har sai da aka biya kudin fansar da ya kai naira miliyan 30, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya rawaito.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.