Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari na tausayin talakawan Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana damuwarsa kan mummunan halin da talakawan kasar  da almajirai ke ciki, inda ya kalubalanci masu ruwa da tsaki da su gaggauta daukar matakan magance matsalar.

Buhari ya bayyana takaicinsa kan yadda almajirai ke yawo da robobi suna neman abinci
Buhari ya bayyana takaicinsa kan yadda almajirai ke yawo da robobi suna neman abinci Arewa aid
Talla

Buhari ya bayyana haka ne a yayin bude bakin azumi tare da mataimakinsa, Yemi Osinbajo da Ministoci da Hafsoshin tsaro da wasu shugabannin hukumomi da cibiyoyin gwamnati a fadarsa ta Villa da ke birnin Abuja a ranar Litinin.

“A duk lokacin da na ke yawatawa a sassan kasar, babban abinda ke damu na sosai shi ne halin da talakawa ke ciki a kasar nan, zaka rika ganin matasa da almajirai da yagaggun tufafi da robobin abinci a hannunsu, suna neman abinda za su ci” in ji Buhari.

Shugaban ya kuma bayyana cewa, neman ilimi ga wadannan mutane nada wahala saboda abu ne mai tsada a gare su, yayinda ya ce, masu ruwa da tsaki a kasar sun gaza domin kuwa akwai bukatar samar da wani shirin bayar da ilimi ga mutanen da ke fama da matsanancin talauci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.