Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 28/01 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 26/01 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 26/01 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 28/01 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 26/01 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 28/01 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 26/01 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 28/01 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 26/01 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 28/01 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 26/01 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 28/01 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 26/01 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 26/01 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 28/01 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 26/01 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 28/01 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 26/01 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 28/01 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Gaggauce

Rahotanni daga yankin Falasdinawa dake Yamma da gabar kogin Jordan sun ce rikici ya barke tsakanin Falasdinawan dajami'an tsaron Isra'ila, bayan da suka tayar da boren nuna adawa da shirin sansanta rikicin yankin da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar. Tuni dai shirin ya samu goyan bayan Firaministan Israila Benjamin Netanyahu, sai dai ya gamu da mummunar suka daga Falasdinawa wadanda suka yi watsi da shi, kuma suka sake jaddada matsayin su na watsi da Amurka a matsayin mai shiga tsakani wajen sasanta rikicin bangarorin biyu.

Najeriya

Buhari ya nemi taimakon MDD kan 'yan gudun hijira

media Shugaba Muhammadu Buhari tare da Maria Fernanda Espinosa ta Majalisar Dinkin Duniya RFI Hausa/Bashir

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi taimakon Majalisar Dinkin Duniya da kuma kasashen duniya wajen tallafa wa tarin 'yan gudun hijirar da kasar ke fama da su da kuma lalacewar kayan more rayuwa.

Buhari ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da shugabar babban zauren Majalisar Dinkin Duniya na zama 73, Maria Fernanda Espinosa wadda ta ziyarci kasar.

Shugaban Najeriya ya ce, yanzu haka kasar na fama da akalla yara wadanda basu san iyayensu ko kuma in da suka fito ba, sakamakon rikicin Boko Haram da ya jefa mutane yankin cikin tashin hankali.

Buhari ya kuma tabo batun tafkin Chadi da kuma yunkurin sake janyo ruwa daga kasar Congo zuwa cikinsa domin farfado da rayuwar mutane sama da miliyan 30 da suka dogara da shi domin rayuwa da sana’oinsu.

Shugabar babban zauren majalisar Maria Espinosa ta yaba wa shugaba Buhari kan shugabancin kungiyar ECOWAS da Tafkin Chadi da kuma rawar da dakarun Najeriya ke takawa wajen ayyukan samar da zaman lafiya a kasashen duniya.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure