Isa ga babban shafi
Najeriya

Mayakan Boko Haram sun karbe sansanin soji a Borno

Mayakan Kungiyar Boko Haram sun karbe wani sansanin soji da ke Jihar Borno a yankin arewa maso gabashin Najeriya, kwanaki kalilan da wani hari ya hallaka sojoji biyar, yayinda 30 suka bace.

Mayakan Boko Haram sun ci karansu babu babbaka a sansanin sojin Najeriya da ke Magumeri a jihar  Borno
Mayakan Boko Haram sun ci karansu babu babbaka a sansanin sojin Najeriya da ke Magumeri a jihar Borno AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Majiyar tsaro ta ce, mayakan haye akan babura da manyan motoci sun far wa sansanin sojin da ke Magumeri mai tazarar kilomita 50 daga birnin Maiduguri a yammacin jiya Jumma’a.

Mayakan sun shafe tsawon sa’o’i 4 suna cin karensu babu babbaka a sansanin, in da suka kwashe makamai kafin daga bisani a yi nasarar fatattakar su.

Mayakan ne suka fara korar sojojin cikin daji bayan sun yi musu barin wuta. Amma kawo yanzu babu rahoton asarar rayuka a harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.