Bakonmu a Yau
Dakta Bashir Kurfi kan rahoton da ya ce Najeriya ce kasa ta shida da al'ummarta suka fi kuncin rayuwa
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:11
Rahoton wani masanin tattalin arziki, Steve Hanke na jami’ar John Hopkins dake Baltimore a Amurka ya fitar, ya sanya Najeriya a matsayin kasa ta shida a duniya da al’ummarta ke cikin kuncin rayuwa.Rahoton ya daura kasashe bisa mizanin tattalin arziki, inda yayi la’akari da abubuwa da dama wadanda idan babu su, kasa na cikin halin ni ‘ya su.Kan haka Micheal Kuduson ya tattauna da Dr. Bashir Kurfi, masanin tattalin arziki a Najeriya.