Isa ga babban shafi
Najeriya

Yan Sanda ke kan gaba wajen cin hanci da rashawa a Najeriya - SERAP

Wani bincike da kungiyar kare hakkin jama’a da kuma tabbatar da gaskiya ta SERAP ta gudanar a Najeriya, ya bayyana cewar rundunar Yan Sandan kasar ce kan gaba wajen aikata laifin cin hanci da rashawa.

Wasu jami'an Yan Sandan Najeriya.
Wasu jami'an Yan Sandan Najeriya. AFP/File/Aminu Abubakar
Talla

Kungiyar tace binciken da ta shafe shekaru 5 tana yi, ya nuna cewa kashi 54 na masu mu’amala da Yan Sanda na bada cin hanci ko kuma na goro, yayinda kashi 63 na Yan Najeriya ke fuskantar kalubalen tambayar su cin hanci duk lokacin da suka gana da Yan Sanda.

Farfesa Akin Oyebode na kungiyar ta SERAP, yace Yan siyasa sun zama masu sace dunkiyar kasa wajen inganta yadda ake satar.

Kungiyar tace wasu bangarori da suka biyo bayan Yan Sandan dangane da shahara aikata laifin na karbar cin hanci da rashawa, sun hada bangaren Shari’a, gudanar da ayyukan gwamnati, bangaren kula da lafiya da ilimi, sai kuma fannin samar da wutar lantarki.

Barista Lawal Ishaq, lauya ne mai zaman kansa a Najeriya, wanda ya ce rahoton na kungiyar SERAP ba abin mamaki bane, inda yace yadda mutane ke jinjinawa jami’in dan sanda mai gaskiya tare da daukaka darajarsa matuka saboda yin fice daga cikin dubbai, hakan a cewar Lauya, alamace da ke nuna yadda aka samu karancin masu gaskiya tsakanin rundunar.

Yayin tattaunawarsa da sashin Hausa na RFI, Barista Lawal Ishaq, ya bada misalin yadda ake yabawa kwamishinan Yan Sandan jihar Kano Muhammad Wakili saboda ficensa kan Gaskiya da rikon Amana.

01:03

Barista Lawal Ishaq kan rahoton matsalar cin hanci da rashawa a Najeriya

Nura Ado Suleiman

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.