Isa ga babban shafi
Najeriya

PDP ta lashe kujerar Gwamnan Bauchi

Hukumar Zaben Najeriya ta bayyana Sanata Bala AbdulKadir Mohammed na Jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Jihar Bauchi, bayan ya samu kuri’u  515, 113, sabanin na Gwamna mai ci Muhammad Abdullahi Abubakar wanda ya samu kuri’u 500,625.

Zababben Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed na jam'iyyar PDP
Zababben Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed na jam'iyyar PDP The Guardian Nigeria
Talla

Alkaluman sakamakon sun nuna cewa, Sanata Mohammed ya bai wa Gwamna Abubakar tazarar kuri’u dubu 14 da dari 488.

Baturen zaben Jihar Farfesa Kyari Muhammad ya bayyana sakamakon, in da yake cewa, “Ni Farfesa Kyari Muhammad, ina tabbatar muku da cewa, nine babban jami’in zaben Gwamnan Jihar Bauchi wanda aka yi ranar 9 ga watan Maris da 23 ga watan Maris, aka kuma kammala yau 25 ga watan Maris, shekarar 2019. Ina mai shaida Bala AbdulKadir Mohammed na Jam’iyyar PDP , wanda ya cika sharuddan da doka ta tanada da kuma samun kuri’u mafi yawa, ya zama wanda ya samu nasara kuma ya zama zababbe."

Gabanin sanar da sakamakon a cikin daren da ya gabata, wata kotun tarayya da ke birnin Abuja ta janye umarninta na dakatar da Hukumar INEC daga tattara sakamakon zaben na jihar Bauchi da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris.

A ranar 19 ga watan Maris ne kotun ta dakatar da INEC daga kammala tattara sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa bayan jam’iyyar APC da Gwamna Abubakar sun shigar da kara.

Kafin dakatar da tattara sakamakon zaben Tafawa Balewa, Sanata Mohammed ya bai wa abokin hamayyarsa tazarar kuri’u dubu 4 da 59.

Tuni dai Gwamna Abubakar ya taya Sanata Mohammed murnar lashe zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.