Farfesa Jibrin Ibrahim kan yadda karashen zaben Gwamnoni ya gudana
Masu sa ido a zaben Najeriya sun bayyana matukar kaduwar su da irin tashin hankalin da aka gani a zaben da aka gudanar a Jihohin Kano da Sokoto da Bauchi da Benue a karshen mako, sakamakon amfani da Yan banga da kuma makamai.
Farfesa Jibrin Ibrahim na Cibiyar Bunkasa Dimokiradiya na daga cikin wadanda suka kalli zaben a Kano, kuma mun tattauna da shi kan irin abinda idan su ya gani, kuma ga tsokacin da yayi akai a tattaunawarsa da Bashir Ibrahim Idris.
A game da wannan maudu'i