Isa ga babban shafi
Najeriya

PDP ta yi taro kan samun shugabancin Majalisar Tarayya

Rahotanni daga Najeriya na cewa, zababbun sanatocin Jam’iyyar PDP sun gudanaar da wani taro a birnin Abuja domin tattaunawa kan rikicin shugabanci a Majalisar Tarayyar Kasar ta 9.

Zauren Majalisar Tarayyar Najeriya a birnin Abuja.
Zauren Majalisar Tarayyar Najeriya a birnin Abuja. RFI Hausa
Talla

Jaridar Daily Trust ta ce, wasu majiyoyi sun shaida mata cewa, taron na cikin shirin Jam’iyyar kan yadda za ta tunkari takarar neman shugabancin Majalisar Tarayyar.

Rahotanni na cewa, zababbun sanatocin na son cimma matsaya kan wanda za su marawa baya daga bangaren sanatocin Jam’iyyar APC a Majalisar, in da suke fatan sake aukuwar abinda ya faru a shekarar 2015, lokacin da Ike Ekweremadu na PDP ya samu kujerar mataimakin shugaban Majalisa duk da rinjayen da mambobin APC ke da shi a zauren.

Ana ganin zababbun sanatocin na PDP za su goyi bayan daya daga cikin sanatocin APC da ke neman shugabancin Majalisar da suka hada da Ahmad Lawan da Ali Ndume da kuma Danjuma Goje da suka fito daga yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Sai dai majiyoyi na cewa, bisa dukkan alamu, zababbun sanatocin na PDP za su fi samun nutsuwa da Goje saboda kusancinsa da Bukola Saraki.

Jam’iyyar PDP na da zababbun mambobi 43, yayinda APC ke da 65 a Majalisar kasar ta 9 da za a kafa nan bada jimawa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.