Isa ga babban shafi
Najeriya

Mahara sun hallaka mutane 10 a Sanga

A Najeriya, akalla mutane 10 suka hallaka a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Nandu da ke karamar hukumar Sanga a jihar Kaduna.

'Yan bindiga sun kai hari kan wani kauyen karamar hukumar Sanga da ke jihar Kaduna.
'Yan bindiga sun kai hari kan wani kauyen karamar hukumar Sanga da ke jihar Kaduna. Information Nigeria
Talla

Harin wanda ake zargin na ramuwa ne, an kaishi cikin daren wannan Juma’a da ta gabata, inda maharan suka kone sama da gidaje 30.

Yayin bada tabbacin aukuwar lamarin, shugaban karamar hukuma ta Sanga, Mista Charles Danladi, ya ce a halin yanzu hankula sun kwanta, kuma jami’an tsaron sun dauki matakan da suka dace, zalika shugabannin al’ummomin yankin sun gana da juna, don rigakafin yiwuwar sake aukuwar makamancin harin na ramuwa.

Tuni dai shugaban Najeriya Muhammdu Buhari yayi tur da harin, tare da bayyana shi a matsayin hanya marar bullewa wajen wareware kowane irin rikici da ke tsakanin wasu bangarori.

Bayaga shan alwashin daukar matakan kawo karshen lamarin shugaban Najeriya ya koka bisa yadda ake siyasantar da kusan komai a kasar, ciki harda kokarin zakulowa ko hukunta wadanda ke da hannu wajen haddasa kisan rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.