Hukuncin kotun mai alkalai uku, ya umurci hukumar zaben ta bai wa Atiku ko kuma wakilansa damar isa ga takardun da aka yi amfani da su ne a kowace rumfar zabe.
Sai dai kotun ta yi watsi da bukatar bai wa wani kamfanin kwararru mai zaman kansa damar isa ga kayayyakin zaben kamar yadda yadda dan takarar na PDP ya bukata.
Atiku ya yi watsi da sakamakon zaben da aka ayyana shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya yi nasara, yana mai zargin yi masa magudi, yayin da jam’iyyar APC mai mulki ta ce, a shirye take ta kare kanta a gaban kotu.
Dokar Najeriya ta bai wa duk mai kalubalantar sakamakon zabe da ya shigar da kara cikin kwanaki 21 daga ranar da aka sanar da sakamako.