Isa ga babban shafi
Najeriya

PDP ta mikawa INEC wasikar korafi

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, ta sake nanata zargin da ta ke yiwa hukumar zaben kasar INEC, na hada baki da jam’iyyar APC mai mulki wajen taimaka mata lashe zaben shugaban kasa na ranar 23 ga watan Fabarairu, da shugaba mai ci Muhammadu Buhari ya yi nasarar zarcewa a wa'adi na 2.

Shugaban babbar jam'iyyar adawa a Najeriya PDP Uche Secondus, tare da Atiku Abubakar, dan takararsu na zaben shugaban kasa.
Shugaban babbar jam'iyyar adawa a Najeriya PDP Uche Secondus, tare da Atiku Abubakar, dan takararsu na zaben shugaban kasa. AFP Photo/PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Korafin na kunshe cikin wasikar da shugaban Jam’iyyar ta PDP Uche Secondus ya mikawa INEC a ranar Talata, domin bayyanawa hukumar bacin rai kan zaben na shugaba kasa da kuma yadda ya gudana a wasu sassan kasar.

PDP ta kara da cewa ce an tafka magudi a zaben ne ta hanyar amfani da jami’an sojoji da ‘yan sanda a jihohin da aka APC mai mulki ta san cewa PDP na da karfin rinjaye, dan haka ta ce za ta bukaci kotun sauraron kararrakin zabe ta bada damar sake tantance kayan aiki da takardun da aka yi amfani da su wajen tattara sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka yi.

Kafin mika wasika dai, ‘ya ‘yan jam’iyyar ta PDP sun soma ne da yin tattaki daga babban ofishinsu da ke Maitama a Abuja, zuwa hedikwatar hukumar shirya zaben Najeriyamai zaman kanta INEC.

Bayan gabatar da korafi kan zaben shugaban kasa da ya gabata, PDP ta kuma gindayawa shugaban hukumar ta INEC, farfesa Mahmood Yakubu sharadin cewa, ya gabatar da jawabin bayyana rashin amincewa da girke jami’an sojoji a kusa da rumfunan zabe, yayin da jama’a ke kada kuri’a a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.