Isa ga babban shafi
Najeriya

Bamu janye aniyar zuwa kotu kan zaben shugaban kasa ba - PDP

Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP, ta musanta rahoton cewa kwamitin kawo zaman lafiya a fagen siyasar kasar NPC, ya sa ta janye kudurin zuwa kotu domin kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 23 ga watan Fabarairu.

Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben kujerar shugabancin Najeriya, Atiku Abubakar.
Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben kujerar shugabancin Najeriya, Atiku Abubakar. REUTERS/Temilade Adelaja
Talla

Shugaban jam’iyyar ta PDP Uche Secondus, ya ce ba shakka kwamitin samar da zaman lafiyar da ke karkashin tsohon shugaban Najeriya Janar Abdusalam Abubakar, ya gana da dan takararsu Atiku Abubakar, amma babu maganar janye kudurin zuwa kotu, illa korafe-korafensu da suka gabatarwa kwamitin.

Secondus ya jaddada bacin ransu kan abinda ya kira cin zarafin masu kada kuri’a yayin zaben na shugaban kasa, a jihohin da aka san jam’iyyar ta PDP na da dimbin magoya baya, da yace sun hada da Rivers, Akwa Ibom, Bayelsa da kuma Cross Rivers, inda matsalar ta fi kamari.

PDP ta kuma bayyana mamakin yadda aka yi, yawan masu kada kuri’ar da suka fita a jihohin Yobe da Borno yayin zaben na shugaban kasa, ya zarta na jihohin yankin kudu maso kudancin Najeriya, duk da cewa wadancan jihohin na fama da matsalolin tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.