Isa ga babban shafi
Najeriya

NOA ta bukaci rage yawan jam'iyyun siyasa a Najeriya

Hukumar wayar da kan jama’a a Najeriya NOA, ta bukaci rage yawan jam’iyyun siyasar kasar, don saukakawa jama’a kada kuri’unsu da ma hukumar zaben kasar, wajen gudanar da aikinta.

Wasu jami'an zabe a Najeriya, rike da takardun jefa kuri'a dauke da alamun Jam'iyyu.
Wasu jami'an zabe a Najeriya, rike da takardun jefa kuri'a dauke da alamun Jam'iyyu. REUTERS/Gbemileke Awodoye
Talla

Bukatar hukumar ta NOA, ta zo ne bayan kammala zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a makon da ya gabata, wanda jam’iyyu 71 suka fafata.

Shugaban hukumar a Jihar Adamawa, Alhaji Ahmad Sudi ya shaidawa manema labarai cewa, an tafka hasarar kuri’u masu yawa a zaben na makon jiya, la’akari da cewa akwai dubban jama’a da suka gaza tantance alamar jam’iyyar da suka so zaba, saboda yawan alamun da ke kan takardar jefa kuri’a, da kuma kamanninsu.

A cewar Sudi, zai iya yiwuwa wasu da suka zabi jam’iyyar PCP da ta zo ta uku a zaben shugaban kasa da yawan kuri’u dubu 110 da 196, sun dauka PDP ce ganin cewa ko a kan takardar jefa kuri’a sunayensu na kusa, hakan kuma zai iya haifar da dangwala musu yatsa bisa kuskure.

Zalika da dama daga cikin wasu da suka zabi ADC da ta zo ta 4 a zaben na shugaban kasa da kuri’u dubu 97, da 874, sun yi zaton jam’iyyar APC ce.

NOA ta kara da cewa yawan jam'iyyun siyasar ya kuma haifar da tsaiko wajen kammala kidayar kuri'u ko tattara sakamakon zabukan da suka gudana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.