Isa ga babban shafi
Najeriya

Dalilin da ya sa ba zan taya Buhari murna ba- Atiku

Dan takarar Jam’iyyar PDP da ya sha kaye a zaben shugabancin Najeriya, Atiku Abubakar ya ce, ba zai yi wa shugaba Muhammadu Buhari murnar lashe zabe ba saboda kura-kuran da ya ce, an tafka a yayin gudanar da zaben na ranar 23 ga watan Fabairu.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar REUTERS/Paul Carsten
Talla

Atiku da ya taba rike mukamin mataimakin shugaban kasa a mulkin Olusegun Obasanjo, ya ce, zai kalubalanci sakamakon zaben da Hukumar INEC ta fitar da ya bayyana Buhari a matsayin wanda ya yi nasara da gagarumin rinjaye.

A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, Atiku ya ce, “ da kamar na fadi ne a sahihin zabe, da tuni na kira wanda ya yi nasara cikin ‘yan dakikoki da samun labarin nasararsa domin taya sa murna”.

Atiku ya kara da cewa, bai taba ganin tabarbarewar demokradiya ba a cikin shekaru 30 na fafutukarsa kamar yadda ya faru a zaben ranar Asabar da ta gabata.

Wannan an zuwa ne bayan shugaban Hukumazr Zabe Mai Zaman Kanta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa, shugaba Buhari ya samu kuri’u miliyan 15 da dubu 191 da 847, yayin da Atiku ya samu kuri’u miliyan 11 da dubu 262 da 978.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.