Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya lashe zaben shugabancin Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari, yayi nasarar lashe zaben shugabancin Najeriya da ya gudana a ranar Asabar 23 ga watan Fabarairu na 2019, nasarar da ta bashi damar zarcewa bisa jagorancin kasar wa’adi na biyu tsawon shekaru 4.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, da yayi nasarar lashe zaben kujerar shugabancin kasar wa'adi na biyu.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, da yayi nasarar lashe zaben kujerar shugabancin kasar wa'adi na biyu. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

A shekarar 2015 Buhari mai shekaru 76, da ya taba jagorantar Najeriya a zamanin mulkin soji, ya samu nasarar lashe zaben shugabancin Najeriya wa’adi na farko.

Alkalumma sun tabbatar da cewa, tun kafin kammala bayyana sakamakon zaben shugabancin Najeriyar a matakin jihohi, Buhari na jam’iyyar APC, ya baiwa babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar tazarar yawan kuri’u kusan miliyan Hudu, matakin da ya haska alamun mawuyaci ne jam’iyyar PDP ta yi nasarar sake karbar mulkin kasar, bayan shafe shekaru hudu da subucewarsa.

Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana sakamakon, inda ya ce shugaba Buhari, ya samu nasarar lashe zaben bayan samun kashi 56 na kuri’un da aka kada, kwatankwacin jimillar kuri’u miliyan 15, da dubu191, da 847.

Dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP, kuma tsohon mataimakin shugaban Najeriyar Atiku Abubakar ne ya zo na biyu a zaben, kamar yadda shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar.

Atiku na biye da shugaba Buhari ne, bayan samun kashi 41 na kuri’un da aka kada, kwatankwacin jimillar yawan kuri’u miliyan 11, da dubu 262, da 978.

A matakin jihohi kuwa, Muhammadu Buhari ya yi nasarar lashen zaben shugabancin Najeriyar a jihohi 19 daga cikin 36, cikinsu har da Legas da kuma Kano, jihohin da suka kafi takwarorinsu a Najeriyar yawan al’umma.

Shi kuwa dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar, ya yi nasarar lashe zaben ne a jihohi 17 da kuma birnin tarayyar Najeriya Abuja.

Zuwa lokacin da muke wallafa wannan labarin, Atiku Abubakar bai bayyana amincewa da sakamakon zaben shugabancin Najeriyar da ya sha kaye ba, wanda a jiya Talata, jam’iyyarsa ta PDP ta bukaci hukumar zaben kasar INEC, ta dakatar da bayyana sakamakon zaben na shugaban kasa, saboda kura-kurai da kuma magudi da ta yi zargin an tafka a cikinsa.

A shekarar 2015, tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya samu yabo daga ciki da wajen kasar, sakamakon yadda yayi gaggawar kiran shugaba Muhammadu Buhari a waccan lokacin domin taya shi murnar lashe zaben shugabancin kasar, bayanda ya fahimci cewa ba zai iya lashe zaben ba, la’akari da alkalumman da suka bayyana, gabannin tabbatar da cewa ya sha kaye.

Karo na 6 kenan da Najeriya ke gudanar da zabukan Dimokaradiyya cikin shekaru 20, lamar da ke nuna dorewar tsarin mulkin Dimokaradiyya bayan kawo karshen mulkin soji a shekarar 1999.

Da farko dai an tsara zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya zai gudana ne a ranar 16 ga watan Fabarairu, zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi kuma ya gudana a ranar 2 ga watan Maris.

Sai dai hakan bai samu ba, domin yayin da ya rage sa’o’i kalilan a soma kada kuri’a, hukumar zaben Najeriyar INEC ta sanar da dage zabukan da Karin wa’adin mako daya, bisa fuskantar matsalolin kammala isar da kayayyakin aikin zuwa wasu sassan kasar, kamar yadda shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu tabbatar, wanda ya ce babu batun Siyasa ko kadan ko wata makarkashiya dangane da matakin.

Dangane da dora sahihancin zaben shugaban kasar da na ‘yan majalisun Najeriyar a mizanin kyawu kuwa, jami’an sa ido kan gudanar zaben na ciki da wajen kasar, sun bayyana cewa an samu ci gaba kan yanayin gudanar da zabukan idan aka kwatanta da na shekarun baya.

Sai dai tawagar masu sa idon da ta kunshi kungiyoyi akalla 70, ta bayyana cewa an fuskanci matsaloli da suka hada da samun tashe tashen hankula a wasu sassan Najeriya da suka I sanadin mutuwar mutane 53.

Zalika wasu jami’an sa idon bayyana cewa an samu wasu Karin matsalolin da suka hada da siyan kuri’a, cin zarafin masu kada kuri’a, da jami’an zabe a wasu tsirarun wurare, sai kuma rashin isar kayan aiki akan lokaci, matsalolin da aka saba gani a zabukan Najeriya da suka gabata.

Matsalolin da kungiyoyin masu sa idon suka zayyana dai za su yi tasiri, wajen yiwa tsarin tattara sakamakon zaben hukumar zaben Najeriya INEC kwaskwarima, ta fuskar soma amfani da fasahar mika sakamakon kuri’un da aka kada kai tsaye daga rumfunan zabe zuwa babban ofishin hukumar INEC da ke Abuja, da zarar jama’a sun kammala zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.