Isa ga babban shafi
Najeriya

Za a sake zabuka a sassan wasu jihohin Najeriya

Hukumar Shirya Zaben Najeriya INEC ta ce za ta bayyana sabbin ranakun da za a sake gudanar da zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar wakilai da dattijai, a wasu yankuna na jihohin Anambra da Rivers da Lagos sakamakon rikicin da aka samu da kuma sace akwatinan zabe.

Wasu 'yan Najeriya a rumfunan zabe, yayin kada kuri'a a zaben shugabancin kasar ranar Asabar a garin Yola da ke jihar Adamawa. 23/02/2019.
Wasu 'yan Najeriya a rumfunan zabe, yayin kada kuri'a a zaben shugabancin kasar ranar Asabar a garin Yola da ke jihar Adamawa. 23/02/2019. REUTERS/Nyancho NwaNri
Talla

Tuni rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama mutane 23 da ake zargi da haddasa hatsaniya a rumfunan zabe, abin da ya kai ga asarar rayukan akalla mutane uku.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Legas, Zubairu Mu’azu ya tabbatar wa manema labara cewa, rundunarsa ta cafke ‘yan jagaliyar siyasa da suka cinna wa kayayyaki zabe wuta a Okoto da Somolu.

Rahotanni sun ce a jihar Rivers inda abin yafi kamari, jami’in soja guda ya rasa ransa, yayin musayar wuta da wasu gungun ‘yan bindiga, kamar yadda kakakin rundunar sojin Najeriya Kanal Sagir Musa ya tabbatar.

Kakakin sojin ya ce gumurzun ya auku ne Abonnema da ke karamar hukumar Akuku Toru, inda ‘yan bindigar suka yiwa sojojin kwanton bauna, yayin da suke sintirin tabbatar da tsaro, bayan maida martani ne suka yi nasarar kashe ‘yan bindigar 6, suka kuma rasa jami’insu daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.