Isa ga babban shafi
Najeriya

An fara fitar da sakamakon zaben Najeriya

An fara fitar da sakamakon zaben shugabancin kasar Najeriya da ke gudana a wannan Asabar bayan rufe wasu rumfunan zabe da dama a sassan kasar.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu KOLA SULAIMON/AFP/Getty Images
Talla

Jami’an Hukumar INEC ne suka bayar da sakamakon zaben bayan kammala kidayar kuri’u a mazabun da ke karkashin kulawarsu.

Koda yake ana ci gaba da kada kuri’u a wasu wuraren samakon tsaikon da aka samu na fara kada kuri’a akan lokaci, yayin da tuni aka rufe wasu rumfuna da misalin karfe biyu na rana agogon kasar.

Miliyoyin ‘yan Najeriya ne suka kada kuri'unsu a zaben wanda ‘yan takarar shugaban kasa 73 ke fafatawa da juna.

Ko da yake hankula sun fi karkata kan manyan ‘yan takara biyu, wato shugaba mai ci Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC mai mulki da kuma babban abokin hamayrsa na PDP, Atuku Abubakar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.