Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya doke Atiku a mazabarsa da ke Yola

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya doke dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a rumfar zabensa da ke Ajiya na birnin Yola a jihar Adamawa.

Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar.
Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar. Sahara Reporters
Talla

Jaridun kasar ciki har da Daily Trust sun ce, shugaba Buhari ya samu kuri’u 186, yayin da Atiku ya samu 167.

A bangare guda, Buhari ya lashe rumfar zabensa da ke Kofar Faru na Gidan Niyam a karamar hukumar Daura ta Jihar Katsina, in da ya samu kuri’u 523, yayin da Atiku ya samu kuri’u uku kacal kamar yadda Jami’in Hukumar INEC mai kula da mazabar, Aliyu Abdullahi ya sanar.

A shekarar 2015, shugaba Buhari ya samu kuri’u 499 a mazabarsa, in da abokin takararsa na wancan lokaci, Goodluck Jonathan ya rasa samun kuri’a ko daya.

Kazalika, shugaba Buhari ya samu nasara a rumfar zaben tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, in da APC ta samu kuri'u 87, yayin da PDP ta samu 18.

Obasanjo ya nuna goyon bayansa karara ga tsohon mataimakin nasa, Atiku Abubakar bayan ya zargi gwamnatin Buhari da nuna gazawa a fannoni da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.